Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya soke shirin yin jawabin ranar Dimukuraɗiyya na bana da zai gudanar a kafafen yaɗa labarai a yau Alhamis.
Tun farko an shirya yaɗa jawabin nasa ne kai tsaye domin tunawa da zagayowar ranar dimokuradiyyar Najeriya wacce ta cika shekaru 26.
A maimakon haka, shugaban zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasa.
An bayyana canjin ne a wata sanarwa da Daraktan yada Labarai da hulda da Jama’a na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Segun Imohiosen ya fitar a daren ranar Laraba.
“Saboda mai girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya shirya halartan taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa, dalilin hakan ya zanyo soke yaɗa jawabin Shugaban kasa a ranar 12 ga Yuni,” in ji sanarwar.
Duk da haka, an bayyana cewa sauran ayyukan ranar Dimokradiyya za su ci gaba kamar yadda aka sanar a baya
Sauran abubuwan da za a gudanar ɗin sun hada da lacca da aka shirya gudanarwa da misalin karfe 4:00 na yamma a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja.
Hafsat Ibrahim


