Tinubu Ya Amince da Sake Bude Iyaka Domin Shigo da Motoci

0
70

Daraktan Sufuri na Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Musa, a jiya, ya bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da sake bude kan iyakar Seme domin shigo da motoci.

Da yake jawabi a taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, taron da aka shirya tsakanin jami’an Najeriya da Benin, Musa ya ce ci gaban ya biyo bayan korafe-korafen masu jigilar kayayyaki da ke aiki a kan iyakar Seme.

Daraktan, wanda ya yi magana a ziyarar da kungiyar ECOWAS ta sa ido a ofishin hadin gwiwa na Seme-Krake, ya ce: “Na kasance a nan tare da tsohon karamin Ministan Sufuri lokacin da masu jigilar kaya suka roki cewa ya kamata a sake bude kan iyakar don zirga-zirgar kaya da ayyuka.

“Tsohon ministan ya sa mu shirya takarda kan hakan. An yi la’akari da shi aka aika zuwa ga gwamnati kuma an gaya mana sabuwar gwamnati ta amince da duk bukatu.”

Shima da yake jawabi, kwamandan hukumar kwastam na yankin Seme, Dera Nnadi yace hukumar ta lura da raguwar kudaden shigarta tun bayan da aka hana shigo da motoci daga kan iyakokin kasa.

Nnadi ya ce: “Tsohon Ministan Sufuri, da yake amsa wasu bukatunmu da masu ruwa da tsaki, ya yi alkawarin kai su Majalisar Zartaswa ta Tarayya, FEC, daya daga cikinsu shi ne yadda za a bude iyakar.

“Ma’aikatar ta sanar da mu cewa an rubuta wa FEC takardar kuma an karbe ta kuma an ba sabuwar gwamnati, ya ba mu tabbacin cewa an amince da duk bukatun.”

Firdausi Musa Dantsoho