Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu Nan take
Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betty Edu nan take.
Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.
Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.
Matakin korar da shugaban yayi ya fito ne daga mai magana da yawunsa Ajuri Ngilale a wata sanarwa da ya fitar a yau.
Hakan ya biyo bayan zargin ka karkatar da wasu kuɗaɗe da za a rabawa al’umma.
Korar minstar na zuwa ne bayan da mutanen ƙasar ke tofa albakacin bakinsu kan nuna bambanci wajen tuhuma ga wadanda ake zargi.
Tun farko al’ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata.
Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata.
Hafsat Ibrahim.