Abinda Yasa Na Cire Naira Miliyan 585 Daga Asusun Gwamnati Zuwa Asusuna-Beta Edu

0
34

Ministar Jin Kai Da Kawar Da Fatara Da Bala’i a Nijeriya Mrs Betta Edu

Har yanzu dai ba a ga karshen badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta gwamnatin tarayya ba, yayin da wata takarda ta bayyana cewa Ministan, Edu Betta ta fitar da N585,198,500.00 a cikin wani asusu na sirri.

A cewar wata takarda mai dauke da sa hannun Edu da aka mika wa ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Ministar ta ba da umarnin a tura N585,198,500.00 ga wani asusun banki mai Oniyelu Bridget

Amma a jikin takardar kuma an nuna cewa an biya kudin tallafin Naira miliyan 585.198 ga marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas, a cikin asusun Oniyelu.

Sai dai da take mayar da martani game da ci gaban, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Ministar Rasheed Zubair ya ce an biya Naira miliyan 585.198 ga marasa galihu.

Ya bayyana cewa biyan kudin tallafin ga asusun wani mutum mai suna Oniyelu Bridget, ya kasance ne saboda shi yana aiki a matsayin Akantanta na Tallafi ga kungiyoyi masu rauni.

Ya bayyana cewa, biyan tallafin Naira miliyan 585.198 an yi shi ne ga marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas.

A halin da ake ciki, wannan ci gaban ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta yayin da ‘yan Najeriya ke mamakin dalilin da ya sa za a biya makudan kudaden gwamnatin tarayya a asusun wani mutum

 

Hafsat Ibrahim