Tinubu ya nemi kuri’u a wurin daurin auren dan gwamnan Gombe

0
202

A ranar Asabar ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya yabawa yankin Arewa maso Gabas bisa gagarumin goyon bayan da suke ba shi a fagen siyasa, inda ya bukaci mazauna yankin da su rubanya goyon bayansu don ganin sun taimaka masa ya cimma burinsa.

 

 Tinubu ya yi wannan roko ne a jawabinsa jim kadan bayan daurin auren Fatiha na Misbau Yahaya, dan gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, da amaryarsa, Amira Babayo, wanda samu halartan sauran manyan baki ciki har da Boss Mustapha wanda ya jagoranci shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari zuwa taron.

 Yayin da yake amincewa da dakatar da yakin neman zaben da akayi, dan takarar shugaban kasa ya yi mamakin dalilin da ya sa aka yi irin wannan ƙuntatawa. Sun ce har yanzu ba a bude kamfen ba, ban san wanda ya rufe shi ba. Muu ‘yan siyasa ne kuma a kullun yakin neman zabe ba a rufe yake ba a wajan mu inji shi.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho