DA DUMINSA : Gini mai hawa hudu ya ruguje a jihar Uyo

0
41

 Wani gini mai hawa hudu da ake ginawa ya ruguje a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

 

 Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san takamamen abun da ya hadasa faruwan haka ba.

 Ginin da ya ruguje yana kan titin Iman daura da titin Nsentip kusa da titin Aka.

 Ginin ya ruguje ne a ranar Asabar da misalin karfe 5 na yamma.

 A cewar shaidun gani da ido, wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun makale a ciki.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho