Dan kasan China mai shekaru 47 ya kashe budurwansa yar kasan Nijeriya da wuka a Kano

0
164

 A safiyar yau ne mazauna jihar Kano suka wayi gari da labarin da ke tayar da hankali a zukatan jama’a da kuma yadda aka kashe wata mai suna Ummita, wadda wani masoyinta Geng Quandong mai shekaru 47 ‘dan kasar China ya daba mata wuka.

 Mummunan sukan wuka da aka yi wa Ummu Khalthum Sani wadda ake kira da Ummita a gida, wanda tsohon masoyinta yayyi, ya yi sanadin kasheta har lahira.

 kafafen sada zumunta sun cika da Hotunan marigayiya Ummita – wanda ke nuna yanayin fuskarta mai cike da annuri, hanci mai kyau, da dimples, murmushi mai haske, sanye da gyale mai ruwan hoda, bakar rigar mai dogon wuya, sanye da ‘yan kunne irin na zinari da abin wuya. Fuskarta cike da alama na ganin wata makoma mai albarka ga kaskantar da kai, ba tare da ta sani ba cewa rayuwanta ya kusa zo karshe nan bada jimawa ba.  

Allah ya jikan ta.

 Rahotanni sun tabbatar da cewa, marigayiya Ummita ta gaji da ci gaba da soyayya da saurayin nata dan kasar china, bayan ta ci gajiyar dimbin arziki daga wajensa.

 Rahotanni sun ce lamarin ya kai har marigayiya Ummita ta hana Geng Quanrong sani ko samun damar shiga gidanta, kuma hakan ya sa ya sha alwashin sanin ta inda take ta duk hanyar da ta dace, wanda daga karshe ya yi nasarar aikata wannan danyen aikin.

 Tunda Ummita ta rasu, kuma wanda ake zargi da kisan dan kasar China yana hannun jami’an ‘yan sandan Kano, bai kamata a wuce gona da iri wajen yin karin bayani kan wannan lamari na kisan Ummita ba.

 Daga: Firdausi Musa Dantsoho