Tafarnuwa tana da amfani ga magunguna domin tana dauke da sinadarai masu amfani ga jiki. Tafarnuwa kuma tana dauke da sinadarin hana kumburin jiki wanda ke da amfani ga jiki. Duk da haka, ana iya amfani da tafarnuwa ta hanyar da ba ta dace ba. A cewar Healthline, akwai kurakurai guda 5 da za ku iya yi yayin amfani da tafarnuwa. A cikin wannan shirin namu na kiwon lafiya, za mu tattauna wasu kurakurai 5 da kuke yi yayin amfani da tafarnuwa don dalilai na magani:
- Shan magani da akayi da Tafarnuwa
Daya daga cikin kura-kurai na yau da kullun shine shan magani na tafarnuwa. Yawancin mutane sun fi son shan maganin tafarnuwa don guje wa warin tafarnuwa. Ko da yake, bincike ya nuna cewa fodan tafarnuwa , magani, ko busassun tafarnuwa ba su da tasirin wajan magani sosai kamar lokacin da take danyanta na yau da kullun.
- Tsarin dafa abinci mara kyau
Kuskure na biyu da mutane ke yi shine lokacin dafa abinci idan suna amfani da tafarnuwa. Yawancin mutane suna sa tafarnuwa lokacin da za su fara dafa abinci. Wannan na iya kashe sinadari na halitta a cikin tafarnuwan, ya kuma kashe amfaninsa. Don haka ana shawartan a ƙara tafarnuwa lokacin da abinci ya kusa karasa dafuwa don kiyaye ƙimar sinadirai.
3.Yawaita Cin sa
Kuskure na uku mafi yawan mutane shine cin tafarnuwa da yawa. Bincike ya nuna cewa a rika cin tafarnuwa 2-3 a kullum. Wannan shi ne saboda tafarnuwa na iya shafar kwayoyin abinci a jikinka saboda yana tattare da antibiotics. Don haka ya kamata a tsakaita cinsa.
- Rashin Amfani da danyan Tafarnuwa
Kuskure na hudu da yawancin mutane ke yi shi ne rashin cin tafarnuwa danye. Tafarnuwa tana da ƙarfi a ɗanyenta don haka ya kamata a ci ta ta zahiri. Wannan zai sa duk abubuwan gina jiki da bitamin da ke akwai su kasance masu aiki.
- Kada Ka Yi Amfani da tafarnuwa Lokacin da kake da Wasu Matsalolin Lafiya
A ƙarshe, Kar ku ci tafarnuwa lokacin da kuke da wasu matsalolin kiwon lafiya. Misali, kar a ci tafarnuwa lokacin da kuke gudawa, idan kuna da matsalar hanta, ko ƙwannafi. Wannan shi ne saboda tafarnuwa na iya haifar da wannan matsala.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho