Wike Ya Soke Filaye 165 A Abuja

0
28

Ministan babban birnin tarayya, Barista Nyesom Wike, ya amince da soke wasu filaye 165 a gundumomin babban birnin tarayya, saboda rashin ci gaba.

Daraktan yada labarai da sadarwa na hukumar babban birnin tarayya Abuja Muhammad Hazat Sule ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar sokewar kamar yadda Ma’aikatar Filaye ta tattara ta samu amincewar Ministan, wanda ya ba da misali da ci gaba da saba wa ka’idojin yarjejeniyar kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Amfani da Filaye ta 1978 a matsayin dalili.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu fitattun mutanen da umarnin janyewar ya shafa sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Udoma Udo Udoma, tsohon gwamnan Kuros Riba, Sanata Liyel Imoke, ministan yankin Neja Delta Ufot Joseph Ekaette, da marigayi mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda-. Ishaya.

Filayen da aka soke na daidaikun mutane ne da kamfanoni, waɗanda suka kasa kiyaye sharuɗɗan yarjejeniyar kamar yadda ya ke ƙunshe a Sashe na 28(5) (a) & (b) na Dokar Amfani da Filaye.

Sauran su ne Jabi (B04); Utah (B05); Katampe Extension (B19); Idu Industrial Area (C16) da Asokoro (A04) gundumomin bi da bi.

Don haka, “Ministan babban birnin tarayya ya yi amfani da ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 28 (5) (a) & (b) na dokar amfani da filaye ta 1978 ya soke sunayen da abin ya shafa saboda ci gaba da saba wa ka’idojin na ci gaban ‘yancin zama na rashin ci gaba,” in ji Sule.

Firdausi Musa Dantsoho