Yan sanda Sun Kammala Binciken Gawar Mawaki Mohbad

0
57

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis ta ce ta yi nasarar kammala binciken da aka yi wa gawar Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

Wannan yana kunshe ne a kafar yadda labarai ta X (wadda akafi sanni da Twitter) na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Rundunar ‘yan sandan ta yi alkawarin bayar da karin bayani ga jama’a da zarar an samu sakamakon.

“Mohbad: Bayanin binciken Gawar, Rundunar ‘yan sandan Najeriya na son sanar da jama’a cewa an kammala aikin binciken gawar Mista Mohbad cikin nasara. Za a ba da ƙarin bayani da zarar an samu sakamakon,” ‘yan sandan sun wallafa a shafin twitter.

A alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tono gawar Mohbad, domin a gudanar da bincike a kan gawar.


Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an fara gudanar da binciken gawar ne domin gano musabbabin mutuwar matashin.

‘Yan sanda sun kuma kama ma’aikaciyar jinya da ta yi wa Mohbad magani kafin mutuwarsa.

A baya dai rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kafa wata tawaga ta musamman domin gudanar da bincike kan mutuwar Mohbad.

Ana sa ran tawagar binciken za ta mika rahoton wucin gadi cikin makonni biyu.

Ayyukan tawagar shine “bayyana yanayin da ke tattare da mutuwar wanda aka azabtar, gano shaidu, masu laifi idan akwai, da duk wani wanda zai taimaka wa tsarin bincike da tura matakai da sauran kayan aikin fasaha don taimakawa tsarin bincike a layi. tare da tanadin da suka dace na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da Dokokin Jihohi.”

 

Mawakin mai shekaru 27, wanda ya kasance tsohon mawakin kamfanin Naira Marley a Marlian Records, ya rasu ranar Talatar da ta gabata.

Firdausi Musa Dantsoho