YADDA AKE HADA SHAYIN ZOBO [HABISCUS TEA]

0
835
White cup of healthy hibiscus tea pouring from the teapot with dried hibiscus flowers on white wooden background, winter hot drink concept for cold and flu

Shi de zobo yana da matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam, kamar yadda Masana sukace zobo musamman bakin nan na temakawa wajen sauko da hawan jini cikin gaggawa saboda yakan bude hanyoyin jini ne ta yadda jinin zai rinka gudanawa yadda ake bukatarsa, ya bayyana cewa yawaita shan zobo na taimakawa wajen rage illar hawan jini a jikin dan adam a sakamakon sinadaran da ke cikin sa.
 Ayau zamu koya maku yadda ake hadda shayin zobo mai daddi.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Zobo
  • Citta
  • Manyan Lemun tsami
  • Lemon grass
  • Karas
  • Star anise
  • Kanumfari
  • Lipton
  • Masoro
  • Siga ko zuma

YADDA AKE HADAWA

  1. Ki wanke lemon grass, karas, kanumfari, masoro, citta, star anise, zobo, da lemun tsamin ki.
  2. A cikin tukunya mai tsafta kisa lemon grass,citta,zobo,star anise, kanumfari, masoro, karas da lemun tsamin ki da kika yanyanka round.
  3. Saiki zuba ruwa ki rufe ya tafasu.                                       
  4. Idan ya tafasu kisa lipton inki ya juku.
  5. Saiki sauke shayin ki, kit ace kisa a cikin kofi.
  6. Sai kisa zuma ko siga kasha lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho