A yawan lokuta muna saurin mu qawata shiri namu domin halartar wani babban taro ko biki amma ba tsammani sai mu fuskanci cewa yanayi na fiskanmu a bushe yake. Wannan matsala ba komi bace a cikin wannan shiri namu zamu kawo muku hanyoyi da dama da fuskarku zatayi sheki da gaggawa.
Mun san cewa akwai abubuwa da dama na ci da shan mu da suka kasance mafi amfani ga gyaran fata namu, don haka zuma ma baa barta a baya ba,duk da kun san cewa abu mai zaki yanada kyau wurin yakar sanyi da kuma shayar da gashin kai. Haka zalika zuma ma yanada fa’idodi da yawa wajen sanya shi a fuska wanda zai sa ku tsaya a gaba gaba wajen taro.
Amfanin zuma guda biyar da yake yi a fuska:
- Yanada matukar amfani in ana wanke fuska dashi kullum
Wanke fuska da zuma na taimakwa magungunan fatar jiki wato yana hade da sinadarin antioxidants haka zalika akwai sinadarin antiseptic da kuma antibacterial wanda ya kasance yana yakar cute kuraje a fata,yana kawar da duk wani baki baki na fuska. Zakayi amfani da ruwan dumi ka wanke fuskanka dashi sai ka debi cokali rabi na zuma sai ka shafa a fuska cikin madaidaicin most kaman na minti 30 kafun ka wanke.
- Zuma asalin maganine wanda bashira illa
Yi bankwana da fatar kanti da ta fita hayyacinta domin ka samu fatarka tayi taushi wajen amfani da zuma na rufe fuska wato a trance (honey scrub) ta yadda zai fitar da fata mai kyau a hankali, hakanan zaka iya hada wasu magunguna kamar avocado, lemo, ko apple cider veneger don habaka fiska a yau da kullum.
- Yanada kyau wajen magance kuraje na fuska
In har abun goge fuska na cleanser yana nuna wani alama na sa kuraje a fuska zuma yanada matukatr kyau a goge fuska dashi,yana taimakawa rage maiko na fuska ,kuma idan aka kasance ana amfani dashi kowane rana zai taimaka wajen kashe kwayoyin cuta na fuskarku, haka zalika yana matukar amfani wajen kawar kesbi na fata.
- Yana saka fuska ya zama da danshi a koda yaushe ba wai a bushe ba
Idan kin kasance fatar ki na da saurin bushewa ko fatarki nada kaushi , yawa shafa zuma yana kauda duk waennan abubuwan, ruwan zuma yana yaki da lalacewa ko kuma gurbacewan abu yana matukar amfani wajen baiwa fata duk wani abu da zai saka shi yayi laushi.
- Yanada kyau ga tsufa
Antioxidants , nutrients da kuma enzymes da suke cikin zuma suna taimakawa wajen inganta fata da kuma ciyar da fata, yana sake saka danshi ba tare da shafa wani mai ba,duk da yake baya kwar da baki baki na fiska gaba daya amma yana rage bayyanar su . Haka zalika antioxidants na taimakawa wajen kawar da duk wata lalacewa na fata wanda shi ne zai iya haifar da alamun tsufa.
BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.