Yadda ake Kwalliyar kananan jakar hannu na zamani (small purses/clutch bags)

0
322

 

Kananan jaka purses ko clutch bags a turance kananan jakukuna ne na mata da babu hannu.jakan  yazama abun kwalliya na zamani da mutane dayawa ke anfani da shi don kara ado a kwalliyan su.  Mutane da dama sun koma anfani da shi a maimakon jaka musamman in za’a fita bukukuwa  kamar su bikin aure, ko suna, dinner, bikin cika shekara ko zagayowar cika shekara da dai sauransu.

Yawanci manyan mata ne ke anfani da shi yanzu kaman matan sarakuna, gaunoni da shuwagabanin kasa  da iyaye. Haka zalika, a wannan zamani, Amare da dama na rikewa a lokacin shagulgulan bikinsu .

Wannan hakan na zuwa ne a kaloli da launuka daban daban.  Ana samun kananan purse da jaka wanda suke zuwa da takalman su design iri daya  masu kyau da daukan idanu,wanda ana kawata shi ne da kayan ado da ake hadawa irin su duwatsu masu launi daban daban kamar su lu’u lu’u da sauran duwatsu masu daraja.

Wasu kananun jakka na zuwa da hanun da ake ratayawa amman wasu basu zuwa dashi.

Suna nan dai a launika da kaloli iri iri,Ana saka shi da ko wani irin kaya.

Amman in an saka shi da  kwalliyar kaya irin na biki,,abin yafi bada armashi

Idan za’a yi anfani da karamin purse toh lallai  Yakamata  a duba a ga ko wani irin karamar jaka ce kuma ko ya dace da irin kalar shigar, yanayin shigar da kuma sha’anin da za aje ayi na ranar.

 

 

Daga: Fatima Muhammad Babamallam