Yajin aiki: ASUU za ta gana da gwamnatin tarayya a ranar Talata

0
48

A yau Talata ne kungiyar malaman jami’o’i za ta gana da wakilan gwamnatin tarayya kan yajin aikin da ta dade tana yi.

Da yake magana a wani shirin siyasa, Shugaban Kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce taron za,a yi shi ne domin tattauna daya daga cikin batutuwa bakwai da ASUU ke nuna rashin amincewa da su.

“WanA yau Talata ne kungiyar malaman jami’o’i za ta gana da wakilan gwamnatin tarayya kan yajin aikin da ta dade tana yi.

Da yake magana a wani shirin siyasa, Shugaban Kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce taron za,a yi shi ne domin tattauna daya daga cikin batutuwa bakwai da ASUU ke nuna rashin amincewa da su.

“Wannan shine batun sake sassantawa,” in ji Osodeke, “sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.

“Ba batun albashi kawai ba ne. Yana da alaka da tsarin, kudade, tsari, cin gashin kai da sauran batutuwa; da yadda ake ba da tallafin jami’o’i.
“Gwamnati ta rage shi zuwa albashi kawai. Amma da a ce sun duba duk yarjejeniyar kuma sun aiwatar da ita, ba za mu yi maganar samar da kudade ba.”

Farfesa Osodeke ya ba da shawarar cewa idan taron na ranar Talata ya yi kyau, za a iya janye yajin aikin.

“Muna shirye mu sanya hannu,” in ji shi.
Daga Firdausi Musa Dantsoho
nan shine batun sake sassantawa,” in ji Osodeke, “sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.