Buhari Ya Kaddamar da Majalisar kawo karshen Maleriya a Abuja

0
37

A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

 

Ana sa ran Majalisar za ta aiwatar da kudurin Gwamnatin Tarayya na kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar.

 

A wajen kaddamar da taron akwai sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari da ministan lafiya Dr Osagie Ehanire da sauran ministoci da manyan jami’an gwamnati.

Daga Firdausi Musa Dantsoho