Yan daba dauke da muggan makamai sun kai hari a majalisar jihar Bauchi tare da jikkata mutane da dama.

0
40

ranar Litinin da daddare ne MAZAN ‘yan sandan jihar Bauchi suka mamaye harabar majalisar dokokin jihar domin dakile tabarbarewar tsaro da zaman lafiya a jihar baki daya.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi yunkurin kona ginin a ranar Lahadi.

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan daba suka far wa wasu ‘yan majalisar a gidansu, inda suka farfasa motoci tare da lalata musu kadarori.

‘Yan ta’addan da yawansu ya kai 50, sun kai farmaki gidan masaukin baki, inda ‘yan majalisar ke gudanar da taro, da ke da nisa da gidan gwamnati, inda suka yi kokarin fatattakan su.

Lamarin dai ya karkata ga rikicin shugabanci da ya dabaibaye Majalisar.

Da yake bayyana abin da ya faru da shi, daya daga cikin ‘yan majalisar da suka samu raunuka a harin, Honorabul Ado Wakili mai wakiltar mazabar Burra ya ce, “Muna cikin   wani taro sai muka ji hayaniya, mutane suna buge kofa. A yayin da muka fito domin ganin abin da ke faruwa, ‘yan iskan sun garzaya wurin rike da bindigogi, da yankan katako da sauran muggan makamai.

“Dukkanmu mun yi kokarin gudu don samun tsira kuma a cikin haka yawancin mu, ciki har da ni, mun ji rauni. Kuna iya ganin fuskata, kusa da idona. Da gaske suke domin a lokacin da muka fito, sun farfasa dukkan motocinmu da tagogin gidan.

” Daya daga cikin membobin Shehu Dan-Ina yayi Allah wadai da aukuwan lamarin. Ya ce ya yi matukar mamaki, toh ina ga lokacin zabe.

Yan sandan da ke gadi a wurin da lamarin ya faru sun ce maharan sun zo ne akan babura dauke da muggan makamai,shi yasa mu ka gudu don mu tsira da rayukan mu,ta haka suka sa mu shiga.

Da ya ke mayar da martani a kan harin da aka kai,mai bai wa gwamna shawara akan al’amurar da ya shafi majalisa ,Alhaji Sani Muhammad Burra, ya faraka  kan shi da lamarin,yayi kira ga jami’an tsaro da su kamo wayanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

Daga Fatima Abubakar