YANZU YANZU: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Nasarawa, Sun Sace Tsohon Mataimakin Gwamna

0
78

 

 

An sace wani tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya tabbatar da sace shi da safiyar yau Juma’a.

Ya ce an sace Gye-Wado ne da safiyar Juma’a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka shiga gidansa da ke kauyen Gwagi da ke karamar hukumar Wamba a jihar.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, an fara bincike ne da wata tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro domin ceto wanda lamarin ya rutsa da shi.

Ga cikakken bayanin ‘yan sanda game da sace shi.

Sanarwar ‘Yan Sanda

Afrilu 7, 2023

CP Maiyaki Baba ya bada Tabbacin Ceton Prof. Onje Yayin da ake haɓaka bincike da ayyukan don ceto shi. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, CP Maiyaki Baba ya tabbatar wa da jama’a musamman iyalan Farfesa Onje Gye-wado cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da wanda  wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance su ba, su ka yi garkuwa da shi a ranar Juma’a, yayin da jami’an ‘yan sanda suka tsaurara aikin bincike da ceto. Bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa a ranar 7/4/2023 da misalin karfe 12:30 na safe wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari kauyen Gwagi da ke karamar hukumar Wamba, suka shiga gidan wani Farfesa Onje Gye-wado inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Bayan samun labarin, sai jami’an ‘yan sandan da ke yankin Wamba suka yi gaggawar zuwa wurin, amma ‘yan bindigar sun gudu da wanda suka yi garkuwa da kafin isowar su. Kwamishinan ‘yan sandan ya kara tattarawa tare da tura dakarun da suka hada da tawagar ‘yan sanda, sojoji, ‘yan banga, da mafarauta na yankin domin ci gaba da neman ceto wanda aka yi garkuwa da shi tare da kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika. Don haka kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga duk wanda yake da bayanai masu amfani da za su baiwa ‘yan sanda damar samun nasarar aikin ceto su kira lambobin waya kamar haka: 09115629178, 09067877096, 08112692680 da 08104441179.

 

Firdausi Musa Dantsoho