Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Taya Sabbin Zaɓaɓɓun Chiyamomi Da Kansiloli Murna

0
16

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Taya Sabbin Zaɓaɓɓun Chiyamomi Da Kansiloli Murna

 

Daga Yunusa Isah kumo

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya taya sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 11 da mataimakansu da kansiloli 114 murna, tare da yin ƙira a garesu su ɗauki zaɓen nasu a matsayin wani nauyi na yiwa jama’a hidima a irin wannan lokaci mai matuƙar muhimmanci.

 

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gomben Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Mujallar Tozali.

 

A sanarwa da gwamnan ya fitar biyo bayan sanarwar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Jihar Gombe GOSIEC ta fitar jiya Asabar, ya taya jam’iyyar APC mai mulki murnar samun gagarumar nasara a zaɓen.

 

Ya bayyana jin daɗinsa da yadda zaɓen ya gudana ba tare da tangarda ba, da kuma yadda masu kaɗa ƙuri’a suka yi zaɓe cikin lumana a lokaci dama bayan gudanar da zaɓen.

 

Gwamnan ya kuma yabawa hukumar zaɓen ta GOSIEC da jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin sauki, wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

 

Gwamna Inuwa Yahaya yace, “Na yaba da yadda masu zaɓe da masu sanya ido da jami’an tsaro da jami’an hukumar GOSIEC da ma al’ummar Jihar Gombe suka kasance cikin tsari a tsawon lokacin da aka gudanar da zaɓen.”

 

Ya ƙara da cewa, “Yayin da nake taya ku murna, ina ƙira a gareku duka, kada ku ga nauyin da masu zaɓe suka ɗora muku a matsayin damar yin aiki kawai, ku yi iya ƙoƙarinku don sauƙe amanar da aka ba ku.”

 

Gwamna Inuwa Yahaya wanda ya bayyana ƙananan hukumomi a matsayin matakai masu matuƙar muhimmanci, ya buƙaci sabin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin su ɗaura ɗamarar samar da ingantaccen shugabanci wanda zai yi tasiri mai kyau ga rayuwar al’umma daga tushe bisa manufofi da tsare-tsaren Jam’iyyar APC da gwamnati mai ci a jihar.

 

Ya buƙacesu su mai da hankali kan riƙon amana, da yin aiki don amfanin jama’a.

 

Idan dai ba a manta ba Hukumar Zabe Ta Jihar Gomben ta ayyana jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomin jihar 11 da kansilolinsu 114.

 

Waɗanda aka zaɓa a matsayin Shugabannin sune:

 

Karamar Hukumar Akko: Mohammed Danladi Adamu

Balanga: Ibrahim Jatau Salisu

Billiri: Madam Egla Idris

Dukku: Adamu Mohammed Waziri

Funakaye: Shuaibu Abdulrahman Adamu

Gombe: Sani Ahmad Haruna

Kaltungo: Iliya Suleiman Jatau

Kwami: Ahmed Wali Doho

Nafada: Babangida Adamu Jigawa;

Shongom: Fatima Binta Bello

Yamaltu Deba: Abubakar Hassan Difa.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim