Hujin Kunne Na Zamani!

0
98

 

Dan kunne kayan ado ne na mata da ake makalawa a hujin kunnen da aka huda don saka dan kunne ko kuma dan kunne da ake mannawa a fatan kunne don kaita kwalliya.

A Zamani yau kwalliyar dan kunne ya saauya inda mata ke huda fiye da hujin kunne daya don kaita kwalliya na masu aji na musamman mai tafiya da zamani. Wasu mata na huda huji biyu, uku, hudu har inda a yanzu ake ganin wasu matan na huda huji goma ko fiye a kunne daya.


Akwai hujin kunne daban-daban a wanan zamanin wada ya hada da standard wato hujin da ake wa ko wace ‘ya mace in an haife ta. Akwai upper lobe, huji daga sama, outter conch daga dan cikin kunne ake huda shi.

Sai transverse lobe da ake hudawa daga kasan kunne da ma sauran su. Ko wace mace na da inda ko kuma huji guda nawa ta ke son yi.

 

Safrat Gani