Jabi Lake and Park : Babban Wajen Shakatawa A Birnin Tarayya Abuja . 

0
226

 

 

 

Jabi lake babban katafaren ruwa ne da ke unguwar jabi dake babban birnin tarayya Abuja, ita jabi lake anyi ta ne domin bada ruwa ga mazauna garin Abuja har kusan mutane dubu dari dake garin amman bayan anyi wannan dam din ta usuman dam dake bwari Abuja, sai aka maida shi wannan jabi lake din wajen shakatawa da shan iska na musamman.

Jabi lake babu nisa da cikin garin Abuja watau central Area ,bai wuce kamar tafiyar minti goma sha biyar ba , haka zalika akwai wajen shakatawa a gefen jabi lake din wanda ake kira da jabi park inda ake zuwa bukukuwa kala kala kamar su picnic, birthday, da ma sauransu.

A gefen jabi lake, ana hango wannan katafaren shahararren wajen siyayya da ake kira shoprite tare da jabi lake mall, ana kuma yin yawo a cikin ruwan lake din watau shigan su jirgi dasu kwale kwale, tare da daukan hotuna.

Inhar mutum mai tsoron ruwa ne, toh basai yaje kusa da lake din ba ma, akwai dawakai da ake badawa haya a hawa ayi yawo cikin park din.

Tabbas jabi lake kyakyawan waje ne tare da iska da bishiyoyi masu ban shan awa . lake dinma shi kanshi na da dadin kallo tare da sanyaya zuciya da kwantar da hankali. Inhar kashigo ko kuma kana garin Abuja, ka yi kokarin zuwa wannan jabi lake and park din domin ganewa idanunka.

Daga Maryam Idris.