Babban hafsan hafsoshin tsaro janar Lucky Irabo yayi kira ga ‘yan Najeriya da su daina saka kayan aikin sojan a wannan lokaci da kasa ke fama da barazanar tsaro, ko da yake bai saba doka ba don nuna so da kauna ce ga rundunar sojin, amma kuma barazana ce ga rayuwar al’umma da lafiyar ta.
janar Iraboh yace miyagun mutane na amfani da kayan don aikata laifuka daban-daban. Ya bada wannan haske ne a lokacin da ya zanta da gidan talabijin na channels a shirin sunrise ta safiyar jumu’a 14 ga janairu 2022.