Ana iya kawo karshen yajin aikin ASUU Gobe– Malamai sun bayar da bayanai

0
60

Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce yajin aikin da suke yi  zai kare nan take idan gwamnatin tarayya ta magance matsalolin su.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana a gidan talabijin na Channels TV’s Politics today a daren Litinin.

 Osodeke ya yi ikirarin cewa an cimma yarjejeniya da gwamnati, amma ba a sanya hannu ba.

 A cewarsa, dagewar ASUU na yin amfani da nasu tsarin biyan kudi, university Transparency Accountability Solution (UTAS), babbar bukata ce.

 “Game da maganar ASUU, ana iya kawo karshen yajin aikin gobe.

 “Mun kammala tattaunawar.  Idan gwamnati ta kira mu yanzu mu zo mu rattaba hannu kan yarjejeniyar, gobe za mu kasance a can.

 “Gwamnati ta gaya mana sun gama gwajin UTAS kuma mun  amince da shi, sannan za mu janye yajin aikin.

 “Yaushe za su sanya hannu kan yarjejeniyar?  Yaushe zasu karbi UTAS?  Wadannan su ne tambayoyi biyu da ya kamata mu yiwa gwamnatin Najeriya,” in ji Osodeke.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho