Da Dumi-Dumin sa:Gobara ta tashi a majalisar wakilai na jahar Kogi.

0
25

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya nan a ginin majalisar dokokin jihar Kogi da ke unguwar Crusher a Lokoja.

Gobarar ta ratsa rufin dakin inda ta yi barna mai yawa a kasan gidan.

Kakakin majalisar, Mathew Kolawole, da mai baiwa jihar shawara kan harkokin tsaro, Kwamanda Jerry Omodara, na daga cikin wadanda suka fara  harabar majalisar in da gobarar ta tashi.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wanda ya san musabbabin gobarar.

Shugaban Majalisar ya ce yana zargin zagon kasa amma za a gudanar da bincike.

Har ila yau dai,majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da ayyukan Dangote a kananan hukumomi biyu.

Majalisar dokokin jihar ta kogi ta zartar da dokar cin gashin kan kananan hukumomin jahar.
Akan rikici kan zargin korar kakakin majalisar Kogi ko yana da alaka da abin da ya faru tsakanin Majalisar da kungiyar Dangote, sai ya ce hakan ya rage ga jami’an tsaro su tantance.

“Yace ya kamata mu bar jami’an tsaro su yi aikin su kuma su ba mu rahoton da ke gaba,” in ji kakakin.

Sai dai wata majiya da ba ta son a buga sunansa ta ce ya yi zargin fashewar wani abu ne amma ya kasa bayyana wanda ke da alhakin kai harin.

Cikakkun bayanai daga baya…

Daga Fatima Abubakar.