Gwamnan babban bankin Najeriya a yau ya ke ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban Kasa.

0
84

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ganawa da gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron na ranar Alhamis shi ne karo na biyu da ke gudana tsakanin su tun bayan da Emefiele ya dawo kasar daga hutun da ya yi a ranar 12 ga watan Janairun 2023.

A ranar Alhamis din na yau ne,babban bankin na CBN na cikin tawagar bankin Larabawa mai bunkasa tattalin arziki karkashin jagorancin Darakta Janar na bankin, Dr Sidi Ould Tah.

Emefiele ya samu goyon bayan shugaban kasa kan sake fasalin kudin Naira da tsarin kayyade kudi da aka bullo da shi a watan Disamba wanda dukkansu ke ganin zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya.

 

Daga Fatima Abubakar.