Michael Mmoh Mai ruwan Najeriya Da Amurka Tauraron Dan Wasan Tennis Ya Sami Tikitin Shiga Gasar Australian Open Zagaye Na Uku

0
22

 

Dan wasan tennis Mai ruwan Najeriya da Amurka mai shekaru 25 a duniya, Michael Mmoh yana cikin mafarki bayan ya tsallake zuwa zagaye na uku na gasar Australian Open ta 2023.

Kimanin awanni 48 da suka gabata, Michael Mmoh ya cika jakunkunansa yana shirin komawa Amurka. A yanzu haka yana shirin sanya $156,775 a aljihu bayan ya tsallake zuwa zagaye na uku a gasar Australian Open bayan da ya fusata dan wasa Alexander Zverev mai lamba 12.

Dan tsohon dan wasan tennis na Najeriya Tony Mmoh, ya yi waje da tsohon dan wasan tennis na biyu Alexander Zverev 6. -7 (1/7), 6-4, 6-3, 6-2 a Margaret Court Arena.

A lokacin da yake fita daga fillin wasan, Mmoh ya rubuta a kan kyamara, “Rayuwa hauka ce.” Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na wasan bayan wasan game da abubuwan da suka faru a kwanakin baya; ya ce ba su “da alaman gaskiya” ya ci gaba da sa ran “karshe ya tashi ko wani abu.”

Mmoh ya ce;

“Sa’o’i 48 da suka wuce gaba daya guguwa ce ta tashi daga shirin komawa gida, nayi sayi tikitin Jirgi, na shirya jakunkuna, jiya zan tafi.

“Yanzu nazo. a nan, kuma na sami mafi kyawun nasara a cikin aikina. Kamar dai ba gaskiya bane. Canje-canjen al’amura guda biyu na gane gaskiya ne kawai”

Zerev a nasa bangaren ya ce kayen da ya yi nuni ne da cewa har yanzu yana da doguwar hanya don samun saukin raunin da ya samu.

Mmoh zai kara da dam wasan tennis na Amurka J.J. Wolf don samun gurbi a zagaye na 16 na karshe a ranar Asabar, 21 ga Janairu.

Daga Safrat Gani