KWALLIYAN AMARE A JAHAR BORNO A RANAR WUSHE WUSHE SU.

0
445

 

Wushe wushe al’adan kanuri ne da akeyi kafin ranar aure. Yawanci ranar juma’a ake bikin. Wushe wushe yana nufin tarban dangin angon yayinda sukazo gidansu amarya ko gurin taron bikin wato (event centre). Biki ne wanda dangin ango da amarya suke zuwa tare dan yinshi. Inda yan uwan ango suke zuwa da makida masu yin kida zuwa gidansu amaryan. Makidan na buga gangansu wato (Ganga kura) da yaran kanuri) wanda kuma yan uwa da abokan arziki suke taka rawa da kuma yiwa amarya da ango likin kudi dama duk wanda yake cikin filin.

A ranan wushe wushen amaryan na saka kayan al’ada wa kwalliyanta kaman riga, zani, abun wuya, abun hanci, da yan kunne, abun hannu dama na kafa. Kuma sunayin kitson al’ada da kunshi a ranar bikin wushe wushen.

Kayan da amarya take sawa a lokacin bikin su ne(Duriya) a harshen kanuri, kayane mai launin ja ne da shudin fari da kore kadan kadan, kayane wanda cikin shi keda fadi haka zalika hanunshi ma nada fadi. Zaninda suke dorawa kuma kala biyu masu maban bantan launika. Yawanci wanda kafi anfani da shi, shine me launin rawaye(wato blue- black) daku ma shudin ja da fari da kuma launin rawaye da baki. Wanda ake daurawa kaman zani wato yadi daya ana kiranshi (Mai yari) da harshen kanuri, haka zalika shi dayan wanda ake daurawa harma ragowa ya rage a rike a hannu wato sama da yadi daya a harshen kanuri a na kiranshi da (Gambara kaji).

A hannu da kafa kuma suna kwalliya da awarwaro na al’adansu mai ruwan azurfa mai kauri wanda ake kira da (Rakka) a yaren kanuri. Haka zalika suna kwalliya da abun hanci wanda suke kira da(“k3ri”) a yaransu,  wasu na zinare ne wasu kuma na karfe dama na azurfa.

Suna kuma kwalliya da sarkan wuya na al’ada wanda suke kira a da (Bugayi da Murzam) a yarensu. (Murzam) yana da dan tsayi wasu yana da igiya daya wasu biyu wasu samada hudu mai launin ja. (Bugayi) kuma igiya ne baki da’ake  zagaje huya, yana da dutse a tsakiyanshi mai launin orange wasu kuma sunasa zinare a tsakiyan dama wasu launin duwatsu daban.haka zalika wasu na karawa da (Toro) wato igiyane baki shima sai de ya banbanta da (Bugayi) saboda shi dagone kuma ana zagaje shine da sisin gwal suke sawa a wuyansu wuyansu.

Kuma hakazalika sunayin kitso wanda ake kira da (“Mbokot3”) a harshen kanuri, wanda kukeyin shi biyu a gaba mai tudu wasu kuma kitso sukuyi mai suna(Nk3la yakk3). Haka zalika da kunshi wato( lalle) a hannu da kafarsu. Bayan angama shirya ta ana daura mata gyalle wanda suke kira da ( Mandil wuriya) ko laffaya a kansu. Bayan angama shirya ta da shigan al’adan su sai danginta su fitarda ita filin taron tare da rakiyan kawayen ta suma da nasu shigan al’adansu wato anko wanda akafi sani da asobi, wasu na shiga na laffaya, ko Dongasho ko Ghana kauwa da ire irensu, dukka sunan kayayyakin da kawayen amaryan suke sawa ne da yaran kanuri. Haka zalika tare da rakiyan baban ninta da kuma inno ninta.

Daga; Rukaiya Umar Digmari