IRE IREN DAN KUNNEN DA AKE ANFANI DASU A ZAMANIN MU NA YAU

0
167

 

Dan kunne kayan ado ne na mata da ake makalasu a hujin kunne inda aka bula. Haka zalika dan kunne kwalliya ne mai mahimmanci ga rayuwan kowa ce ya mace dake haska fuskansu da kwalliyan su na yau da kullum.

  Dan kunne yana zuwane ta bangare daban daban

_ Akwai dan kunnen karfe

_ Akwai na robber

_ Akwai na azurfa

_ haka zalika akwai na zinari da lu’u lu’u.

Na Daya: chandelier(wato dogon dan kunne)

Yana daya daga cikin dan kunne da ke jan hankalin mutane kuma yana bada kamanni mai kau saboda launinsu. Mafi yawanci mata masu son kele kele sunfi anfani dashi sabo da sunfi so insunyi kwalliya suja hankalin mutane garesu a duk inda sukaje.Hak azalika dogon dan kunne yana haska mata masu suffan fadin fuska da mata masu masa kaicin fuska da kuma masu suffan zuciya.Dogon dan kunne yana zuwa ne yawanci da launin dawasu masu kel’ keli a jikinshi. Haka zalika dogon dankunne akwai mai dan fadi da kuma siriri sosai ya danganci wanda mutum keso yayi anfani ma kwalliyanshi.

Na Biyu: Hoops

Dan kunne dayake zagaye daga gaban kunne zuwa bayan kunne. Wanda yake barin rami atsakanin dan kunnen da kunnen. Dan kunne mai huji wato hoops yana zuwa ne iri daban daban wato mai kauri da kuma siriri. Dutse dayake zagaye da dan kunnen yana kyalkyali kaman de launin lu’u lu’u kuma yawancin su basu da nauyi. Haka zalika yanayin kau ga mata masu masakai’cin fadin fuska.

Na ukwu: Clip- ONs

Clip- ONs dan kunne ne wanda akafi sani da mai makulli. Shide wannan dan kunne yana da ma kulli. Shide wannan dan kunne yana da makullin shi da zaka rufe dan kunnen bayan kin sakashi. Haka zalika anfi anfani ma yara kananu saboda karya fadi. Shide wannan dan kunne clip-ONs wato mai mukulli azagaye yake wato(round). Haka zalika tsoffofi ma suna yawan anfani dashi sabo da yajima a kunne bai fadi ba sabo da mukullinshi. Clip ONs yana da kau kuma yana da saukin farashi.

Na hudu: Studs

Studs wanda akafi sani da dan kunne manne shine sanannen dan kunne wanda akafi sani. Dan kunne ne mai duwasun launin lu’u lu’u, matsakaici mai dadin anfani. Yawanci yan mata masu hujin kunne sama da daya nayin anfani dashi a sauran huji nan kunnensu. Studs dan kunne ne mai kau kuma yake haska kwalliyan mata.

BY RUKAIYA UMAR DIGMARI