Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su fara karbar tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 daga hannun jama’a nan take.
Duk da haka, ta sanya madaidaicin adadin da bankuna za su iya karba a kan N500,000.
Babban bankin na CBN ya ci gaba da cewa tsofaffin kudaden ba su da wata doka.
Wata majiya daga bankin ta ce CBN ya umurci bankunan da su karbo kudaden maimakon zuwa ofishin CBN sakamakon matsalolin da suka samu wajen shiga bankin.
Wani jami’in CBN ya ce, “Ku je bankin ku amma ku cika fom kafin ku je. Ku tafi tare da lambar aje kudi da zaka samu. lambar ne, bankuna za su karba daga gare ku. Amma idan ya zarce 500,000, za ku je CBN ku ajiye shi.”
A ranar Alhamis ne gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, ya umurci bankunan da su samar da tsofaffin takardun kudi na N200 ga ‘yan Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya ce tsohuwar takardar kudi ta N200 za ta kasance a kan doka har zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023, yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya da su ajiye tsoffin takardunsu na N500 da 1000 a CBN.
Sai dai zanga-zangar da ta yi ta tada jijiyoyin wuya a jihohi daban-daban dangane da karancin kudaden da ake samu na Naira, ya sa CBN ya umarci bankunan da su karbo manyan kudade bayan ganawa da shugabannin bankunan.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho