Wani dan sanda da har yanzu ba a tantance ba a Mopol 8 Jos, jihar Filato, an rahoto cewa ya harbe wani matashi a ranar Lahadi, inji jaridar The PUNCH.
Wanda harba mai suna Nyommena Badapba, mazaunin unguwar Tudun Wada, an harbe shi ne a kafadarsa jim kadan bayan gardama da dan sandan.
Wani mazaunin unguwar Tudun Wada da ya shaida harbin ya tabbatar wa da jaridar News Point Nigeria da ke Jos afkuwar lamarin a ranar Lahadi.
A cewarsa, dan sandan da matashin sun yi ta cece-kuce a kan wanda zai lashe zaben gwamna a jihar.
Shaidan ya ce, “Dan sandan yana kunshe dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress, Dr Nentawe Yilwatda.
“Ya ce ba zai ci zabe ba saboda ba shi da wani abin da zai baiwa al’ummar jihar amma Nyommena na kokarin kare shi.
“Lokacin da gardama ta yi zafi, aka shawarci saurayin da ya daina magana, ya tafi gidansa.”
A cewar wanda abin ya shafa, dan sandan da ke dauke da makamai ya bi bayan matashin.
“Ba zato ba tsammani, dan sandan ya auna kansa ya bude masa wuta amma aka yi sa’a harsashin ya afka wa matashin a kafadarsa.
Ya kara da cewa “Yanzu haka yana asibitin koyarwa na jami’ar Bingham da ke Jos inda aka garzaya da shi.”
A cikin wani hoto da ke yawo a yanar gizo kuma wakilinmu ya samu, an ga matashin a kwance kan gado da bandeji a kafadarsa da hannunsa.
Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta da suka mayar da martani ga hotunan sun kalubalanci rundunar ‘yan sandan jihar Filato da ta kama dan sandan da ya harbe matashin.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, da aka tuntube shi ya ce har yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho