Matar Tinubu Ta Kaddamar da Shirin ECoN a Kano, Don Haɓaka Ƙirƙire-Ƙirƙire da Tattalin Arziki

0
16

Matar Tinubu Ta Kaddamar da Shirin ECoN a Kano, Don Haɓaka Ƙirƙire-Ƙirƙire da Tattalin Arziki

Daga Hafsat Ibrahim | 23 ga Afrilu, 2026

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da shirin Energise Commercialisation Now (ECoN) a Jihar Kano, inda ta bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin ƙirƙire-ƙirƙire a ƙasar nan tare da bunƙasar tattalin arziki ta hanyoyin daban-daban.

Da take jawabi a wajen ƙaddamarwar  Sanata remi  ta ce shirin ya yi daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ke bai wa fifiko kan masana’antu, fasahar zamani, ƙera kayayyaki, harkokin kirkire-kirkire, da kuma bunƙasa sababbin dabaru.

Ta jaddada muhimmancin sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da fitar da ɗanyen kaya zuwa gina tsari mai tallafawa kuɗaɗen bincike, faɗaɗa kasuwanci, da kuma juya kirkire-kirkire zuwa abin da zai amfani al’umma domin samun ci gaba mai ɗorewa da kuma gogayya a duniya.

A cewarta, Najeriya na da dimbin baiwa da kirkira, inda ake samar da sabbin dabaru kullum daga jami’o’i, cibiyoyin bincike, cibiyoyin kirkire-kirkire da kuma matasa. Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, ta ce masu kirkire-kirkire na Najeriya na sukayi   fice a duniya, musamman a bangaren fasahar kuɗi (fintech) da bunƙasa kasuwanci.

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen haɓaka harkokin kasuwanci, samar da ayyukan yi, da ƙara yawan kuɗaɗen shiga na ƙasa (GDP), tare da jaddada muhimmancin bai wa mata da matasa dama domin a samu cigaba mai haɗa kowa da kowa.

“A wannan lokaci, cikin yardar Allah, na kaddamar da shirin Energise Commercialisation Now domin amfanin dukkan ‘yan ƙasa, farawa daga yankin Arewa maso Yamma zuwa sauran yankuna na ƙasar nan,” in ji ta.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana zaɓen Kano a matsayin wurin ƙaddamar da shirin a matsayin wajen da amincewarsu da ƙoƙarin jihar wajen jagorantar sauyi na kirkire-kirkire a Arewacin Najeriya.

Ya ce an tsara shirin ne domin cike gibin da ke tsakanin bincike, kirkire-kirkire da kasuwa.

Gwamnan ya kuma bayyana matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin ƙarfafa tsarin mulki na zamani (digital governance), ciki har da kafa Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano, faɗaɗa kayan aikin ICT, da kuma farfaɗo da ilimin kimiyya da fasaha.

Tun da farko, Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Udeh, ya bayyana ƙaddamar da shirin a matsayin wani babban ci gaba wajen mayar da kimiyya da fasaha ginshiƙai na bunƙasar tattalin arziki.

Ya lura cewa duk da Najeriya na samar da ingantattun bincike da kirkire-kirkire, yawancin sakamakon ba su kai kasuwa ba saboda ƙarancin damar samun jari da kasuwa.

Daga karshe Taron ya samu halartar manyan baki masu daraja, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, Gwamnan Jihar Jigawa, da wakilan gwamnoni daga jihohin Kebbi, Katsina, Sokoto, Kaduna da Zamfara. Haka kuma, matan gwamnoni na jihohin Arewa maso Yamma bakwai, tare da ‘yan majalisar wakilai, sanatoci, ministoci da sarakunan gargajiya sun halarta.