Tsohon Gwamnan Osun, Oyetola ya taya Adeleke murnar nasarar A Kotun Koli

0
34

 

TSOHON gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Talata wanda ya tabbatar da zaben Sanata Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar.

 

“Ga gwamnan Osun, Sanata Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ina amfani da wannan damar domin taya ka murnar nasarar da ka samu a kotun koli,” in ji Oyetola a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa.

 

“Yayin da nake yi maka addu’ar Allah ya sa wa’adin ka ya kawo cigaba ga al’ummarmu da jiharmu , ina rokon ka da ka mayar da hankali wajen samar da shugabanci na gari.”

 

Da yake ajiye siyasa a gefe, tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai sanar da magajinsa cewa dole ne matslahar talakawa ta fi komai muhimmanci ba tare da takurawa ko nuna wariya ba ta hanyar siyasa ko akida ko addini.

 

“Duk wani bambance-bambance na sirri da muke da shi dole ne ya ba da hanya ga ci gaban babbar jihar mu. Dole ne a tabbatar da tsaron mutanen Osun ba tare da la’akari da addini da siyasa ba. Ina yi maka addu’ar zaman lafiya da ci gaba,” inji shi.

 

A cewarsa, duk da cewa hukuncin da kotun kolin ta yanke ya saba wa muradun ‘ya’yan jam’iyyarsa da magoya bayansa, amma ya amince da hakan ne domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

 

Oyetola ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyarsa ta APC, da magoya bayansa, da wadanda suka zabe shi a zaben gwamna da aka yi a ranar 16 ga Yuli, 2022 da su amince da hukuncin a matsayin ikon Allah kuma su ci gaba.

 

“Mun yi imani cewa mun gabatar da kara mai kyau a gaban Kotun Koli amma Kotun ta yi tunanin akasin haka kuma ta yanke hukunci. Duk da cewa sakamakon ya sabawa burinmu da na ’yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu, duk mun amince da hakan a matsayinmu na ‘yan kasa masu bin doka da oda,” inji shi.

 

“Ga mambobinmu da magoya bayanmu a fadin jihar nan, ina kira gare ku da ku amince da hukuncin da Kotun ta yanke kuma ku ci gaba. Halin da ake ciki yanzu shine nasara a gare mu. Yana hade da asara da nasara cikin daya. Yayin da muka rasa Osun, mun ci Najeriya.”

 

Tsohon gwamnan wanda ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya bayansa da kada su ji bakin ciki ko damuwa kan hukuncin da kotun ta yanke, ya kara musu kwarin guiwa da su himmatu wajen gudanar da ayyukan da ke gaban jam’iyyar. Ya kuma yabawa shugabannin jam’iyyar a jiha da kasa baki daya bisa jajircewa da goyon bayan da suka bayar a tsawon lokacin rikicin doka.

 

“Na ci gaba da jajircewa wajen ci gaban jihar Osun. Don haka zan ci gaba da yin aiki tare da ’yan Osun, kungiyoyi da cibiyoyi masu kishin kasa don samar da ci gaban jiharmu mai daraja,” inji shi.

 

“Hakazalika, ina kira ga daukacin al’ummar Osun da su ci gaba da nuna dabi’ar Omoluabi da kuma tabbatar da burin magabatanmu na jihar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

 

Firdausi Musa Dantsoho