Muhimman Abubuwa 4 da Ya Kamata namiji Ya mallaka Kafin Ki Yarda Ki Aure Shi.

0
702

 

 Sautin kalmar “aure” yana da kyau da annashuwa. Yana kuma nufin hadin namiji da mace  tare da fatan shawo kan wahalhalu tare a matsayin mata da miji da kuma kasancewa cikin rayuwar jin dadi har abada a matsayin mata da miji.                           

 zamani ya canza da za a ba da budurwa  aure ba tare da la’akari da ko saurayin ya dace da  ita ta kowace hanya ba. Iyalan budurwar sun fi damuwa da cewa ta kai mizilin  yin aure. A wannan halin da ake ciki, tana iya yin sa’a ko rashin sa’an mijin aure. A sakamakon haka, za ta dage da nuna farin ciki  koda tana shan wahala.

Amma, kamar yadda yake a yanzu, abubuwa suna canzawa cikin sauri. Kuma abubuwa ba daya suke ba kamar yadda suke a da. A sakamakon haka, zaku iya ganin budurwa wacce ta kai yin aure tana ɗaukar lokacinta don gujewa yin zaɓin da bai dace ba na abokin zama a kwanakin nan.

 

A sakamakon haka, a matsayin ki na mace, ga abubuwa guda hudu da dole ne namiji ya kasance dasu  kafin ki yarda ki aure shi;

  1. Ka tabbatar yana sonki da gaske:Mutumin da yake ƙaunar ki da gaske zai yi tunani sau biyu kafin ya cutar da ke ko ma ya yaudare ki. Zai fifita ki domin ya damu da ke da kuma alakar da ke tsakanin ku. Lokacin da kika auri mutumin da ba ya son ki, ba zai yi jinkirin bibiyan yan mata  tare da yaudarar ki da kusan kowace mace kyakkyawa da ta zo masa ba. Kafin ya cutar da ke kuma ya tozarta ki ga wahalar da tsananin damuwa, ba zai yi nazari ba. Amma  idan yana ƙaunar ki da gaske,  za ki zama abu mai ƙima a gareshi wanda ba zai so yayyi asara ba.

  1. Dole ne ya kasance mai tunani da nazari yadda ya kamata: Kamar yadda ake cewa, ba a ayyana balaga ta mutum da shekarunsa. A sakamakon haka, kawai saboda mutum ya bayyana yana da shekaru 30 ko 40 baya nuni da cewa ya balaga kuma yana iya magance ƙalubalen rayuwa. A sakamakon haka, a matsayina ki na budurwa, dole ne ki kasance mai lura da alamun cewa yana da nasari, tunani,  kafin ki yarda ki aure shi. Idan akasin haka ne, laifin ki ne.

  1. Dole ne ya kasance yana da hanyar samun kudin shiga na halal: Lokaci ya wuce da ake tilasta wa  budurwa shan  wahala tare da mutumin da take so ta aura. A wannan zamani, dole ne ku tabbatar da cewa yana da ikon kula da ku da yaran ku. ku tabbatar cewa zaku iya kula da kan ku ko yana kusa ko baya kusa.

  1. Dole ne ya zama mutum wadda zai fahimce ki:Fahimtan juna yana da muhimmanci tsakanin masoya. Za a yi ta fuskantan matsaloli a kai a kai idan babu fahimta. A sakamakon haka, dole ne ki tabbatar cewa ya fahimce ki kamar yadda kika fahimce shi ta fuskokin abubuwan da yake so da abin da ba ya so. Lokacin da kuka fahimci juna da abokin tarayya za ku iya magance matsaloli yayin da suka taso maku.           

 

By: Firdausi Musa Dantsoho