DA DUMI-DUMINSA: Gobara ta tashi a sansanin sojin sama dake Abuja

0
31

WUTA ta kone wasu sassa na sansanin sojojin saman Najeriya dake kan titin filin jirgin sama a babban birnin tarayya.

Har yanzu dai ba a gano musabbabin tashin gobarar ba a lokacin da ake hada rahoton.

Jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya ma sun yi kokarin kashe gobarar.

Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar sojin saman Najeriya kan lamarin.

Zaku samu karin bayani ba da jimawa ba….

 

Firdausi Musa Dantsoho