Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa a baya bayan nan cutar Diphtheria wato mashaƙo ta kashe yara sama da ɗari biyar da Ashirin 520.
Daraktan asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF Dr Muhammad Nasir Mahmoud ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai daya gudanar yau Talata.
Inda ya qara da cewa daga watan Desambar 2022 zuwa yauzu an samu rahoton yara dubu 8900 na wadanda ake zargin sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatar da yara 6300 suka mutu.
Ya qara dacewa cutar ta zagaya jihohi 36 da kuma kananan hukumomi 44 da jihar Kano ke da shi.
A cewarsa, yara 27 cikin ɗari ne kawai aka yiwa rigakafi yayin da kaso 7.5 na yaran jihar ba su yi rigakafi ba,sannan kaso 59.9 cikin Dari biri basu da kariya kuma kaso 5.5 cikin Dari ba a ma san suna dauke da cutar ba.
Daga Fatima Abubakar