Rundunar ‘yan Sandan jahar Filato ta cafke Noah Kekere da ake zargin shi da cire sassan jikin majinyata a asibitin shi ba tare da sanin su ba.

0
23

Rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ta cafke wasu likitoci guda biyu bisa zargin su da hada kai da wani likita mai suna Noah Kekere, da ake zargi da cire sassan jikin marasa lafiya ne ya girbe muhimman sassan jikin dan adam.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, shi ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Jos.

Alabo ya ce wadanda ake zargin tare da Kekere a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da bincike a kansu.

A kwanakin baya ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta kama Noah Kekere, bayan an zarge shi da cire kodar ta wata mata a lokacin da ake yi masa tiyata.

 

Daga FatimaAbubakar.