Kisan Ummita:Kotu Ta Yanke Wa Frank Geng Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

0
34

Kisan Ummita:Kotu Ta Yanke Wa Frank Geng Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa Dan China FrankGeng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya mutu.

Idan zaku tuna dai, a ranar 16 ga watan satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka ummita, mazauniyar Unguwar jambulo a Jihar Kano.

Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji yanke masa hukuncin ne bayan tabbatar da hujjojin da Masu gabatar da Kara suka yi a gaban kotun.

 

 

Hafsat Ibrahim.