DA DUMI-DUMI: Jirgi mai saukar Ungulu dauke da Shugaban Kasar Iran da ministan harkokin kasar Ya Yi hatsari.

0
22

 Ana Ci Gaba Da Binciken Jirgi Wanda yake Ɗauke Da Shugaban Ƙasar Iran Da Ministan Harkoki Waje Ya Faɗi A Gabashin kasar.

Jirgin Mai Ɗauke Da Shugaban Ƙasar Iran Da Ministan Harkoki Waje Ya Faɗi ne a Gabashin Azarbaijan

Ministan harkokin cikin gidan kasar Iran Ahmad Vahidi ya tabbatar da cewa wani jirgin sama mai saukar Ungulu dauke da shugaban kasar Ebrah…

Ministan harkokin cikin gidan kasar Iran Ahmad Vahidi ya tabbatar da cewa wani jirgin sama mai saukar Ungulu dauke da shugaban kasar Ebrahim Raeisi ta fadi a birnin Jolfa da ke lardin Gabashin Azarbaijan na arewa maso yammacin kasar Iran.

Jirgin mai saukar Ungulun na jigilar shugaban kasar Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da gwamnan Azarbaijan ta gabas, Malek Rahmati, da wasu fasinjoji da dama, a lokacin da suka gamu da matsala, inda aka tilasta masa yin “saukar gaggawa” a kusa da Jolfa, wani birni mai iyaka da kasar Azarbaijan.

Lamarin ya faru ne a dajin Dizmar da ke tsakanin garuruwan Varzaqan da Jolfa.

Bayan sa’a daya da faruwar lamarin, kungiyoyin agaji sun isa yankin inda suka fara gudanar da bincike.

Tawagar ceto ta mutum 20 aka tura yankin, amma saboda tsananin gurbatar yanayi, musamman hazo, aikin bincike da ceto zai dauki lokaci, in ji hukumomi.

Haka nan na’urori marasa matuka suna taimakawa da aikin gaggawa wajen binciken.

Wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu dauke da wasu ministoci da jami’ai sun isa wurin lafiya.

Shugaba Raisi yana dawowa ne daga bikin kaddamar da madatsar ruwa a kogin Aras tare da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev.

 

Hafsat Ibrahim