Muhammadu Sanusi ll ya ce da an bar batun rarraba masarautu a Kano, to da an ci gaba da rarraba masarautu a jihar kenan.
”Da an bar wannan lamari na rarraba masarautu to da wata rana sai an naɗa Sarkin Fagge, ko Kunci ko Kumbotso”, in ji shi.
Dan haka sabon sarkin ya ce ‘yan majalisa da gwamnatin sun ceto tarihi babba wanda yake haɗa kan al’umma.
Muhammad Sanusi II ya ce sarki ba ya fadanci ba ya kirari amma yana faɗar gaskiya, yana mai cewa lalle gwamnan jihar ya cika gwarzo.
Sarkin ya kuma gode wa gwamna da al’ummar Kano.
Muhammadu Sanusi II ya ce babu wani wanda yake da wani gida a masarautar Kano duk zuri’ar Dabo ɗaya ce wanda shi ne ya kafa masarautar Kano.
Haka kuma sabon sarkin ya ce ba zai tofa komai ba a kan waɗanda suka cire shi saboda a cewarsa ba su isa komai ba.
Hafsat Ibrahim.