Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce sun bi dukkan ƙa’idojin da suka dace wajen soke dokar masarautun jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a gidan gwamnati, a lokacin miƙa takardar kama aiki ga sarkin Kano na 16, inda ya ce ba sa jin tsoron kowa tunda akan ƙa’ida suka yi wannan Garanbawul
Gwamnan ya mika masa takardar aiki ne a wani takaitaccen biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano ranar Juma’a.
A jawabinsa na mika wa Sanusi takarda a ranar Juma’a, gwamnan ya ce, ba sabon sarki aka naɗa ba, “kujerarsa da ya tafi na wucin gadi ne yanzu muka dawo masa da ita.”
Sanusi ya ci gaba zama sarkin Kano ne shekara hudu bayan tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tube shi a 2020.
An tube shi a lokacin ne shekara shida da hawansa kan karagar da marigayi Sarki Ado Bayero ya bari a shekrar 2014.
A lokacin ne gwamnatin Ganduje ta kirkiro tsarin masarautu biyar a jihar, ta kuma nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
A ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024, Majalisar Dokokin Kano ta kammala gyaran fuska ga dokar masarautun jihar, inda ta soke dukkan masarautun biyar da aka kirkiro a zamanin Ganduje.
Daga karshe Gwamna Abba ya rattaba hannu a bisa dokar ya kuma da ba wa sarakunanan masarautun wa’adin sa’a 48 su fice daga fada.
Sai dai gwamnan ya mikawa sarki Sanusi II takardar kama aiki bayan da wata kotun tarayya dake zaman ta a Kano ta dakatar da aikatar da sabuwar dokar da ta bada damar nada Muhammad Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Kuma haka siddan ba za mu lamunci wani alkali yana can wata ƙasar ya bayar da umarnin a kan abin da muka bi ƙa’ida ba”, inji Abba Kabir Yusuf.
Sarki Muhammadu Sanusi II ne zai jagoranci sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnatin jihar, ba kamar yadda aka tsara a baya cewa a masallacin kofar kudu zai Jagoranta ba.
Hafsat Ibrahim