Hudubar Sarkin Sanusi na II yayin da ya jagoranci sallar Juma a ,a masallacin fadar Kano 

0
55

Hudubar Sarkin Sanusi na II yayin da ya jagoranci sallar Juma a ,a masallacin fadar Kano

 

Alhaji Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano na 16, ya ce babu wanda ya isa ya tambayi Allah dalilin da yasa ya gudanar da duk wani al’amari da ya aiwatar.

 

Sarkin ya bayyana haka ne a cikin hudubarsa ta sallar juma’a wadda ta jagoranta babban masallacin cikin gari Kano.

 

Hudubarsa ta ta’allaka ne akan imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau.

“Duk wanda ya yarda cewa Allah ne kadai ke bayar da komai, kuma ya yarda da cewa babu mai tambayar Allah dalilin da yasa yayi komai.

“An gaya mana cewa duk wanda bai yarda da kaddara daga Allah take ba, imaninsa bai cika ba. Ya kamata mutum ya kasance mai godiya a lokacin yanayi mai dadi da mara kyau. Dole ne mu yi imani cewa duk abin da ya faru da mu kaddara ce daga Allah.

 

Yan Sanda sun magantu kan shirin Sarki Aminu da Sarki Sanusi na yin sallar juma’a a masallaci guda

“Muna gab da kusantar Zhul Hijja wanda yake da fa’ida sosai kuma dole ne mu kiyaye addu’o’i a cikin kwanakin masu albarka .”

 

Daga bisani sarkin shi ne ya jagoranci sallah.

Idan za a iya tunawa mun rawaito da safiyar wannan rana ta juma’a cewa sarki Sanusi da Sarki Aminu zasu gudanar da sallar juma’a a masallaci guda, sai dai daga bisa ta ce kowanne cikin Sarakunan zasu gudanar da sallar juma’ar ne a inda suke.

 

 

Hafsat Ibrahim