Sarki Sanusi ne zai jagoranci sallar Juma a ba Aminu ba- Rundunar Yan sandan kano ta kuma yi gargadin game da yada labaran karya.

0
6

YANZU-YANZU: Rundunar ‘yan sanda a Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi na biyu zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a, maimakon Sarki Aminu Bayero.

 

Kwamishinan ‘yan sanda Usaini Gumel a Yau Juma’a ya ce Aminu Ado Bayero zai halarci sallar Juma’a a masallacin da ke cikin fadar Nasarawa, inda a yanzu haka yake.

 

Shugaban ‘yan sanda a Kano ya jaddada cewa, za a samar da kwararan matakan tsaro a fadar Sarkin Kano domin gudanar da sallar Juma’a a ƙarƙashin jagorancin Malam Sanusi, Tare da goyon bayan hukumomin tsaron jihar.

Yace, “’Yan sanda suna kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin karya da labaran karya da ke yawo a shafukan sada zumunta, su rika gudanar da ayyukansu ba tare da fargabar zage-zage ko tsoratarwa ba.

 

“’Yan sanda za su ci gaba da samar da tsaro da ya dace don tabbatar da hakan zai ba wa mazauna yankin damar gudanar da Sallar Juma’a cikin kwanciyar hankali ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyinsu ba.”