Kano/Tsafta/Tallafi/Adamu
*TSAFTAR MUHALLI: Hukumar Lura da Kwashe Shara ta Jihar Kano ta Horas da Mata 160 Yadda Za su Rika Sarrafa Shara……*
Daga Adamu Muhammad Bichi
Hukumar kula da tsaftar muhalli tare da kwashe shara ta jihar Kano wato REMASAB tare da hadin gwiwar taimakekeniyar lafiya ta jihar, ta kaddamar da wani shiri na horaswa ga mata dari da sittin (160).
Shirin zai horas da kuma bayar da tallafin ga matan domin juya shara ta koma dukiya.
Yawan zubar da shara barkatai na daya daga cikin kalubalen da Jihar Kano ke fuskanta, a yayin da ake samar da sama da tan 300 a kullum, wanda ke haifar da dumamar yanayi da kuma toshe magudanan ruwa.
A bisa haka ne Gwamnatin Jihar karkashin hukumar lura da tsaftar muhalli da kwashe shara ta samar da wani shiri na horas da mata da kuma tallafa musu da kayan aiki domin tsaftar muhalli.
Shugaban hukumar dakta Muhammad Khalil ya ce an samar da shirin ne domin ya dace da tsareren Gwamnatin Jihar na shawo kan matsalar yawan shara a fadin jihar.
An tsara shirin yadda zai taimaka wajen tsaftar muhalli da kuma dogaro da kai.
An dai rabawa wadanda su ka ci gajiyar shirin su 160 kayayyakin aiki da suka hada da bukitan kwashe shara da safar hannu, da sauran kayayyaki
Wallafawa Hafsat Ibrahim kawo




