Masoyan Sanata Barau I. Jibrin Maliya Sun Yi Barazanar Gurfanar da Masu Danganta Shi da Ta’addanci

0
13

Wasu da ke bayyana kansu a matsayin masoyan DSP Barau I. Jibrin Maliya sun bayyana cewa ba za su zura ido ana yi wa jagoransu ƙazafi da ɓata suna ta hanyar danganta shi da ta’addanci ba tare da wata hujja ba.

A cikin wata sanarwa da Khadija Muhammad (Ummi), wadda aka bayyana a matsayin jagorar ‘yan gwagwarmaya kuma Tauraruwar Sarkin Maganin Ƙasar Hausa, ta fitar, kungiyar ta ce ta kuduri aniyar bin duk wata hanyar doka domin gurfanar da duk wanda ya yi irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe a gaban hukumomin da suka dace.

Kungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan zarge-zarge na iya bata sunan mutum tare da haifar da rudani a cikin al’umma, saboda haka ba za su lamunci ci gaba da yaɗa su ba.

Haka kuma, ta yi kira ga hukumomin tsaro da na shari’a da su gudanar da cikakken bincike kan duk masu yaɗa irin waɗannan zarge-zarge, tare da binciken duk wanda ake zargin yana ba su mafaka ko kariya.

A cewar kungiyar, tana da cikakken yaƙinin cewa gaskiya za ta bayyana, kuma doka za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da hannu wajen yaɗa bayanan ƙarya ko aikata duk wani laifi.

Kungiyar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da barin hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike daidai da tanadin doka