Ambaliyar ruwa ta fitar da mazauna Nasarawa daga gidajen su

0
14

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Nasarawa ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta shafi mutane kasa da 361,000 a kananan hukumomi takwas cikin 13 na jihar.

Babban Sakataren Hukumar NASEMA, Zachary Allumaga, a ranar Alhamis ya bayyana cewa jihar Nasarawa na daga cikin jihohin da hukumar Metrological Agency ta Najeriya ta yi hasashen za a fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a watannin Satumba da Oktoba.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho