Shugaba Buhari yayi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a wannan shekaran

0
37

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a kasar kafin karshen wannan shekara.

Buhari ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi a bikin Olojo na 2022 a Ile-Ife, jihar Osun.
Shugaban kasar wanda ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya wakilta, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a daina satar mutane da fashi da makami kafin karshen wannan shekara.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da tsaro a koda yaushe, kada su bar aikin ‘tsaro ga yan sanda su kadai.
“Haka zalika hakkinmu ne a matsayinmu na mutane kada mu bar tsaron al’ummarmu ga jami’an tsaro kadai.
Dole ne dukkanmu mu yi taka tsantsan kuma mu sa ido a abubuwa na daban dake faruwa a cikin al’ummarmu. Gwamnati na sane da kokarin da kuke yi na tabbatar da hadin kai a fadin kasar nan, dole ne in tabbatar muku da cewa duk wani nau’in rashin tsaro da ke addabar kasar nan za su zama tarihi kafin karshen shekara.”

Buhari ya bukaci cibiyoyin gargajiya da su magance matsalar karancin abinci a kasar ta hanyar jawo hankalin matasa su koma gona.
“Kabiyesi, wannan cikakkiyar al’ada ce da ake nunawa, ina alfahari da kasancewa a nan kuma na kasance cikin ingantaccen al’adar . To, a zamanin da, wannan biki ya kasance wani ɓangare na girbin noma, don haka, ya bukaci cibiyar gargajiya da ta jawo hankalin jama’a su koma gona. Kamata ya yi mu rungumi aiki tukuru, mu hada shagali da aiki don zama wadda za’a girba da inganci,” in ji shi

Daga Faiza A.gabdo