‘Ya’ya suna daya daga cikin abu mai muhimmanci da suke wanzar da farin ciki acikin iyali ko zuri’a,samunsu na daya daga cikin rahmar Allah da ke saka iyaye farin ciki marasa misaltuwa.Akwai mutane dayawa da suke neman yara ido rufe ,basu nan basu can,asibitoci iri iri da shan magugunan gargajiya, wasu har kaucewa suke da zuwa gidajen malamai kawai domin su samu ‘ya’ya da zasu iya kira da nasu.Haifan yaro babban abu ne, haka zalika kulawa da yaron da aka Haifa shima wani abu ne daban mai matukar muhimmanci ,sau tari iyaye dayawa sun dauka siyo kayan abinci da siyowa yara kayan sakawa da biyan kudin makaranta sune kawai hakkokin da yakamata su sauke akan yaransu, amman banda wannan, akwai abubuwa da dan yawa daya kamata iyaye suyi ma yayansu da ya zarce iya siyan masu kayan sakawa da kuma biyan kudin makaranta kawai.wannan kadai basu isa sauke hakkin da Allah ya rataya a wuyan iyaye ga yaransu ba.
Shi tarbiyan yaro yana kara wahala ne daga lokacin da yaro yafara yin abota da mutanen waje wadanda ba irin tarbiyan su daya ba. A matsayin iyayen masu son inganta tarbiyan yaransu, dole ne su damu in har yaro yafara kawo wasu dabi’u na mutane ko abokai da bai dace ba daga waje , tarbiyan da ba a kan daidai suke ba kuma wadan da basu dace ba. Sau dayawa, yaro yakan fara abota da mutanen waje ne tun daga farawarsa makaranta,kamar daga noziri,firamare da su karatun sakandare har jamia, kuma zai hadu da mutane da abokai daban daban wadanda suke da tarbiya da hali daban daban.da kuma yadda suka dauki rayuwar gaba daya ba iri daya ba ne.
A zahiri, abota tsakanin yara matasa na daya daga cikin abubuwanda ke saka yara canzawa daga halinsu na kwarai zuwa wani hali da bashi bane tarbiyan iyayen ba, sau dayawa tarbiyan yaro yakan canza a dalilin yin abokai daga bangarori dayawa na rayuwa. Daga yanayin Magana, zuwa yadda suke saka kaya, zuwa yadda ake aski da dai sauransu.
A bisa wannan dalilin ne yakamata iyaye su saka ido akan irin abota yaransu keyi, su san abokan yaransu da kuma kalar tarbiyansu harda iyayen abokan yaran nasu kamar yadda muka ce a baya.
Kula da tarbiyan yaro ya wuce kula da abinci da yake ci kawai, a a, ya kunshi kula da addininsa, maganarsa, abubuwanda yake kallo, abinda yake sakawa a kwakwalwarsa da sauransu, tarbiyantar da yaro yafi gyara wa gurbataccen tarbiyan yaro sauki , haka zalika sanin abokan yaro sosai yana taimakawa wajen gane yadda tunanin danki yake sarrafuwa, kuma zai taimaka wajen gane wani irin abokai yakamata yayi da wadanda baikamata yayi ba, watau abokan da zasu iya taimakawa kenan wajen gurbata tarbiyan yaranki.Yana kuma da muhimmanci iyaye su san mene da mene abokan yara da yaran sukeyi, su sanya masu ido sosai, in sun fita ina sukaje, wani wasa sukeyi, hirarrakin su da ma sauran su. Wasu yaran sukan nuna tarbiyya mai kyau tare da abokansu a gaban iyaye wanda abu ne mai kyau, amman a bayan idonsu kuma abun babu dadi, a saboda haka ne yake da matukar muhimmanci a saka masu ido sosai a waje da cikin gida baki daya
Yara halittu ne masu sanyaya zuciya ga iyaye, kuma kiwo ne Allahu yabamu, kuma zai tambayemu akansu akan irin tarbiyan da muka basu, muzama masu baiwa yaranmu muhimmanci da kulawa sosai, saboda a rashin wannan shine mataki na farko dake janyo wa yaro yin abokai dakuma biye wa Magana da shawarwarin mutane a waje da inba ayi sa’a ba, ake samun gurbataccen tarbiya bisa ga irin gurbatacen shawara da zai iya bi.
Daga Maryam Idris