Ayyuka 4 da ke koya wa yaro yadda ake rubutu

0
130

 

Rubutu baiwa ce mai mahimmanci wacce ke buƙatar aiki da yawa.  Yayin da yaro ke wucewa ta kowane mataki na girma,  suna haɓaka iyawa tare da yin rigiman amfani da fensir kuma tare da yin koyo,  ya kamata yaran ku su iya yin zane-zane da fensir.

Lokacin koyawa yaronka rubutu, yana buƙatar ƙarfin hannu, da ingantacciyar daidaituwar gami da hangen nesa, sarrafawa, da daidaita idanu-hannu.

Anan akwai ayyukan da za su iya taimaka wa yaro wajan haɓaka ƙwarewar da yake buƙata a rubutu

 

 1 Gina kayan wasan yara

Ka ba wa yaronka horo da yawa tare da gina kayan wasan yara domin wannan zai bunkasa tsokokin  hannunsa da yatsunsa, yana sauƙaƙa masa wajan kama kayan aikin rubutu.  Hakanan zai iya inganta daidaituwar ido da hannun yaranku.

2 Yi amfani da allon tsaye,  ko takarda da aka makala a bango, don aiwatar da zane da rubutu:  Wannan yana ƙara ƙarfin wuyan hannu da kafada da kwanciyar hankali, wanda ke taimakawa wajen haɓaka ingantaccen damar motsa jiki da hannu.

 3 Gabatar da wassan jifa da kamawa

Waɗannan wasannin za su iya inganta daidaituwar ido da hannun yaranku.  Kuna iya gabatar da wasanni kamar jefa ƙwallo cikin kwando ko jefawa kallo da kamawa.

 

 4 ku yawaita barin yaranku fita waje

Ƙarfafawa yaro ya ba da lokaci a filin wasa saboda ayyukan da suka haɗa da hawa, rarrafe, da ja da kai duk suna taimaka wa yara su haɓaka ƙarfin jiki da kulawa lokacin rubutu.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho