Menene shayarwa?
Shayar da nono lokacin da ake ciyar da jariri madaran nono, kai tsaye daga nono. Ana kuma kiranta raino. yanke shawarar shayar da nono lamari ne na mutum. Haka zalika yana iya jawo ra’ayoyi daga abokai da dangi. Yawancin kwararrun likitocin, ciki har da Cibiyar Nazarin Ilimin Yara na Amurka (AAP) da Kwalejin Kwararrun Likitoci da Likitocin mata, suna ba da shawarar sosai ga shayar da zallan Ruwan nono na musamman, babu madaran gwangwani, ‘ya’yan itace, ko ruwa na tsawon watanni 6. Ko Bayan fara basu wasu abinci, sun ba da shawarar ci gaba da shayar da nono a gabaki daya farkon shekaran jariri.
Sau nawa ya kamata ku shayar da jariri nono ya danganta da ko jaririn ya fi son cin abinci kadan, ko akai akai ko yana daukan lokaci mai tsawo wajan cin abinci. Hakan zai canza yayin da jaririn ku ke girma. Jarirai galibi suna son cin abinci kowane sa’o’i 2-3. Idan suka kai watanni 2, suna cin abinci kowane sa’o’i 3-4 , kuma idan suka kai watanni shida, yawancin jarirai suna ci abinci a kowane sa’o’i 4-5. Ke da jaririn ki na musamman ne, kuma shawarar Shayar da nono ya rage gare ki.
Alamomin da ke nuna Jaririnki Yana jin Yunwa
Daya daga cikin hanyoyin da za ku fi sanin cewa Jaririnku suna jin yunwa shine kuka. Sauran alamun da ke nuni da cewa jaririn ku na bukatar abinci sun haɗa da:
*Lasar leɓunansu ko fitar da harshe
*Motsa bakin su, ko kan su don neman nono.
*Saka hannun su cikin bakin su.
*Bude bakinsu
*Tsotsar duk abun da yazo kusa da bakin su abubuwa.
Amfanin shayar da zallan Nono Ga Jariri
Madarar nono na samar da abinci mai kyau ga jarirai. Yana da kusan cikakkiyar hadin bitamin, furotin, kitse dama duk abin da jaririnku ke buƙata ya girma. Kuma duk an bayar da shi a cikin tsari mafi sauƙin narkewa fiye da tsarin madaran gwangwani. Madarar nono tana ɗauke da sinadirai wanda ke taimaka wa jaririn yaƙi da ƙwayoyin cuta na bacteriya. Shayar da nono yana rage haɗarin kamuwa da ciwon asma ko rashin lafiyan.
Haka kuma, shayar da zallan nono na musamman ga jariri na tsawon watanni 6 na farko, ba tare da wani tsari ba, yana kawo kawar da matalar ciwon kunne, cututtukan numfashi, da kuma zawo. Yana kuma rage tafiye -tafiyen zuwa asibiti ganin likita.
An danganta shayar da nono da kara ƙimar ƙwaƙwalwa mafi girma a cikin ƙuruciya a lokacin karatun. Haka zalika, kusancin jiki, fata-da fata, da kallon cikin kwayan ido duk suna taimaka wa jaririn ku kara kusanci da ku, kuma ku sami kwanciyar hankali. Jarirai da ake shayarwa sun fi samun nauyin da ya dace yayin da suke girma maimakon zama yara masu kiba. AAP ta ce shayarwa kuma tana taka rawa wajen rigakafin SIDS (cutar mutuwar jarirai kwatsam). An bayyana cewa yana rage haɗarin kamuwa da ciwon sukari, tsananin kiba, da wasu cututtukan daji, amma ana buƙatar ƙarin bincike akan haka.
Amfanin shayar da zallan Ruwan Nono Ga Uwa.
Shayar da jariri Nono yana ƙona ƙarin adadin kitse, don haka zai iya taimaka muku rage kiba da kukayi lokacin da kuke da ciki da sauri. Yana fitar da sinadarin oxytocin, wanda ke taimakawa mahaifa ta koma yanayin girmanta na da kafin daukar ciki kuma tana iya rage zubar jinin mahaifa bayan haihuwa. Shayar da nono kuma yana rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mama dana mahaifa. Yana iya rage haɗarin ku na kamuwa da osteoporosis.
By:Firdausi Musa Dantsoho