An bai wa yan kasuwar panteka makonni biyu da su fice daga Mabushi ko su fuskanci fushin hukuma.

0
88

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, ta bada wa’adin makonni biyu ga ‘yan kasuwar Pantakers na Mabushi da su fice daga wuraren da suka shahara da aikata laifuka ko kuma su ruguza yankin ba tare da jin kai ba.

Babban mataimaki na musamman kan sa ido da tabbatar da tsaro ga ministan babban birnin tarayya, Comrade Ikharo Attah ne ya bada wa’adin ranar Juma’a a Abuja a wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyar ‘yan kasuwar Gwan-Gwan Mabuchi.

A cewarsa: “Bayan sati biyu duk abin da ya rage a yankin za a ruguje shi ba tare da tausayawa  ba. Amma za mu tsaya tsayin daka tunda kun daukaka kara, kuma za mu isar da sakonku ga Ministan amma ku tabbatar kun  tattara komatsan ku kafin  sati biyu idan ba haka ba za mu ruguza komai.

“Malam Muhammad Musa Bello ya umarce mu da mu dakile tare da tsaftace duk wani maboyar masu aikata laifuka a cikin babban birnin kasar nan, ba tare da wata tangarda ba.

Hakazalika, Mataimakin Darakta a Hukumar Kula da Muhalli ta Abuja (AEPB) Kaka Bello ya ce, za mu ba su  makonni biyu amma za mu tabbatar da bin ka’ida.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Gwan-Gwan Mabuchi, Salisu Rabi’u ya roki a kara musu lokaci domin su hada kayansu masu tsada, sannan gwamnati ta samar musu da wani wurin da za su yi sana’arsu ta halal.

DAGA Fatima Abubakar.