An ceto wasu mutane 14 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin Kaduna.

0
54

Dakarun sashe hudu na Operation Whirl Punch da na musamman na bataliya ta 167 na sojojin Najeriya sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan ya fitar a ranar Asabar, ya ce sojojin sun fara sintiri daga dogon zango zuwa yankin Tukurua da ke karamar hukumar Chikun ta jihar inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.

Ya ce an kashe daya daga cikin ‘yan fashin yayin da wasu suka gudu.

“Sojojin, a yayin aikin, sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da maza tara da mata biyar,” in ji Aruwan.

“An kai wadanda abin ya shafa zuwa wani wuri mai tsaro don tantancewa  kafin a sake hada su da iyalansu.”

Aruwan ya kara da cewa sojojin sun lalata sansanoni da dama a yayin fafatawa da ‘yan bindigar.

Ya kara da cewa, “An gano babura biyu a yayin aikin.

Kwamishinan ya ce gwamnan Nasir el-Rufai ya ji dadin nasarar da sojojin suka samu, ya kuma yaba musu.

 

Daga Fatima Abubakar.